Spread the love

Bishop na Divine Seed of God Chapel Ministry Sasa Ojoo dake Ibadan Fasto Wale Olagunju ya yi hasashen abin da za su faru a shekarar 2020 daga farkonta zuwa ƙarshe a lamurran Nijeriya.

Fasto Olagunju ya sanar da hasashen abubuwa 48 da yake sa ran faruwarsu a wannan shekarar ya ƙara tabbatar da hasashensa na shekarar 2016 cewar mulki zai ci gaba da zama arewa shekara 12.

Fasto Wale ya yi hasashe ƙwarai a cikin manyan jam’iyyun biyu da manyan ‘yan siyasa masu buƙatar addu’a a Nijeriya.

Fasto ya ce Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya yi addu’a sosai don ganin ya kammala wa’adin mulkinsa a ofis.

Ya kuma shawarci Tambuwal ya yi addu’a kar a tsige shi.

Wannan bayanan sun fito ne a jaridar The Sun ta ranar Lahadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *