Kungiyar kiristocin Nijeriya CAN sun jefar da kalaman sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar, na cewa kiristoci ba su cikin kowace dannewa na hana su yin addininsu a kasar nan.

A cewar CAN mai alfarma Sarkin musulmi bai yi masu adalci ba na kauda kansa ga irin mamaye su da ake yi da kuma nuna masu fifiko.

Sarkin musulmi ya ce ya kadu ga kalaman da kungiyar kiristoci ke yi na cewar ana hana kiristoci yin addini a kasa.

CAN sun goyi bayan kasar Amerika da ta sanya Nijeriya cikin kasashen da ke hana mabiya addini aiwatar da addininsu.

Sarkin musulmi ya yi kalamansa ne a wurin rufe taron kungiyar dalibai musulmi ta Nijeriya a jami’ar Bayaro Kano karo na 77 da ake yi duk shekara, ya ce kalaman CAN karya ce da son rai.

Ya ce Ta’addanci da wasu bata garin Fulani makiyaya ke yi bai shafi addini ba, hasalima ba dukkan fulani ne musulmai ba.

Ya ce akwai kiristoci Fulani kamar yanda akwai Fulani musulmai.

Martanin CAN daga shugabansu na yankin Arewa Rabaran John Hayab ya ce abin mamaki ne mai alfarma baya son ya fuskanci abin da yake zahiri.

Ya ce akwai hujja kan maganarsu in aka dubi rashin daidaito a harkar siyasa, tattalin arziki, shugabanci a kasar nan musamman a arewacin Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *