Spread the love

‘Yan kasuwa na jiran rattaba hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari a daftarin kudi da haraji majalisar tarayya ta aminta da shi da ake ganin gwamnatin tarayya za ta yi amfani da shi wajen samun kudi a shekarar 2020, masu hulda da Bankunan Nijeriya da masu ruwa da tsaki sun yi magana kan nauyin da suke gani a wurin amfani da nambar haraji TIN ga hada-hadar Bankuna da abokan huldarsu.

Amfani da nambar yana cikin shirin da ake da shi na tabbatar da ‘yan Nijeriya sun biya haraji ga gwamnati, an tsara a daftarin dokar duk wani da zai ajiye kudi ko hulda da banki ko bude asusun ajiya tau sai da nambar haraji waton TIN.

Dakta Uju Ogbunka ya ce ana iya samun koma baya ga harkar hada-hadar banki in ba a samu wayar da kan mutane ba da har za su iya taimakon gwamnati ga biyan harajin da bukatar gwamnati za ta biya.

Ya ce in ka dubi hulda ta banki ana iya samun ci baya domin wasu mutane ba su iya biyan haraji kan haka suna iya rufe asusun ajiyarsu ko ma su bar shi bude amma su nemi wata hanya ta ajiyar kudinsu, kar ka manta mutane suna iya sayen kayan ajiya musamman ma ‘yan kasuwa da suke iya ajiye kudinsu a kasuwanci, maganar gaskiya kafin wannan lokacin haka mutane ke yi, wasu mutane suna iya yanke shawarar su sayen duk abin da suka ga dama.

Malam Shehu Mika’il ya ce tsarin ci-baya ne gare su musamman bankuna domin mutane za su daina son amfani da banki, a misali masu karbar Fansho da ba su san komai ba kan tsarin kawai suna zuwa ne su karbi kudi su wuce.

Ya ce yafi dacewa gwamnati ta saurarawa wannan tsarin in dai har da gaske tana son mutane su cigaba da amfani da tsarin bankuna na zamani, saboda yin wannan tsarin zai kori abokan hada-hadar banki.

Ya ce abar masu kula da harkar haraji ta kasa su nemi wata hanya ta karbar haraji yafi a kawo wata rigima bayan wadda ake ciki. A cewar shugaban kungiyar Constance a zantawarsa da daily SUN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *