Spread the love

Akalla mutum shidda aka kashe da wasu uku da suka samu rauni a harin da ‘yan kungiyar Boko haram suka kai ga al’ummar jihar Borno.

Sun kai hari a kauyen Kwagilim dake cikin karamar hukumar Chibok a kudancin jihar Borno.

Majiyar ta ce Boko haram sun yi wa kauyen kawanya da misalin karfe shida na marece a lokacin da mutanen wurin ke shirin tafiya Coci don aikata ibadar Kirsimeti.

Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya tabbatar da faruwar lamarin a ziyarar da ya kai a Uba a karamar hukumar Askira-Uba a kusa da Chibok a jiya.

“Abin mamaki a jiya Boko Haram hara a Kearagilim karamar hukumar Chibok in da aka kashe mutum shidda, uku suka samu rauni.”

Zulum ya bayyana haka a lokacin da yake yi wa wasu shugabannin jam’iyarsa ta APC bayani a Uba.

Kwamishinan ma’aikatar kula da radadin talauci Nuhu Clark ya ce maharan sun tafi da mace biyu, kuma dukan wadan da suka samu rauni su uku an kai su asibiti suna karbar magani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *