Spread the love

Tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Kanal Sambo Dasuki ya ce ba shi da wata jikakkiya da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan tsare shi da ya yi shekara hudu da suka wuce duk da umarnin kotuna na a sake shi.

Dasuki ya yi magana ne a lokacin tattaunawa da gidan rediyon Amerika sashen Hausa(VOA) jim kadan bayan an sake shi ya dawo gida.

An tambaye shi ko tsare shi nada alaka da rawar da ya taka a wurin kife gwamnatin shugaba Buhari a 1985.

Dasuki ya ce “Ban da wata masaniya kan haka, abin da kawai nasani duk abin da Allah ya tsara sai ya faru.”

“Bani da rashin jituwa da kowa, nafi karfin in kullaci wani, ban da matsala da kowa duk abin da ya samu mutum daga Allah ne haka ya tsara.”

Dasuki ya ce a shirye yake ya je kotu kan kare kansa da abin da ake zarginsa ya bar zuwa kotu ne a farko saboda an ki aminta da umarnin kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *