Shahararar ‘Yar wasan Hausa da sunanta ya daɗe yana yawo a masana’antar shirya finafinnai ta Kannywood Saratu Giɗaɗo wadda aka fi sani da Daso ta ce tana wasan kwaikwayo ne ba don faɗakarwa da ilmantarwa ba sai don kuɗi kawai.

Daso a hirarta da BBC Hausa ta ce “Na ɗauki sana’ar fim matsayin kasuwanci ba faɗakarwa ko ilmantarwa ba. A da da muke cewa muna faɗakarwa ba mu isa mu yi kuskure sai a riƙa cewa mun ce muna faɗakarwa, ilmantarwa amma abin da ta ke ko shi ke yi to yanzu Business muka ɗauki fim”. A cewar Daso.

Wannan kalamai sun bayyana tunanin ‘yan fim a yanzu kuma kusan shi ne ra’ayinsu in ka dubi takonsu da mu’amalarsu da tsarin labaransu.

Daso ta tona asirin ra’ayin ‘yan fim da suke ɓoyewa domin tsoron tofin alatsine wanda ita Dason ba ta gudun hakan ga al’ummar Hausawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *