Ba abin da ‘yan Nijeriya za su yi murna da shi, sakon ASUU ga Buhari

Shugaban kungiyar malaman jami’a na kasa Farfesa Biodun Ogunyemi a ranar Laraba ya ce talakan Nijeriya ba abin da zai yi wa murna a lokacin bukin Kirisemeti.

Farfesa ya ce halin da kasar ke ciki ba wani dadi ga rayuwar talaka a lokacin da masu kudi ke kara arzirta kansu.

Shugaban kungiyar ya fadi haka a sakon da ya aikawa mambobin kungiyarsa kan bukin kirisimati.

Ya yi kira ga mambobinsa da su kalli kalubalen da ke gabansu a sabuwar shekara.

A cewarsa gurbacewar tattalin arzikin Nijeriya na kara matsar da talakan kasa abin da ke hana shi more bukin kenan.

Ya fahimci bukin zai zama mai amfani a wajen talaka in ya samu ingantaccen ilmi da kiyon lafiya da sauran bukatunsa na rayuwa yanda yake so.

kalaman shugaba kenan kamar yadda jaridar daily trust ta kawo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *