Tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Kanal Sambo Dasuki an sake shi daga wurin da hukumar DSS take tsare da shi in da ya share sama da shekara hudu a tsare.

Dasuki yana tsare tun daga watan Yunin shekara 2015.

Da marecen Yau Talata ne hukumar DSS ta sake shi a Abuja bayan umarnin gwamnatin tarayya da ta ba su.

Manyan lauya Ahmed Raji ya tabbatar da sakin Sambo Dasuki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *