Spread the love

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce har yanzu ba ta kai matsaya ba kan ranar da za a bude iyakokin Nijeriya na kasa.

A watan Agustan da yagabata ne aka rufe bododin kan iyakar da suke da makwabtaka da kasar Chadi da Nijar da Benin da Cameroun, aka shirya wani karfaffan sintiri domin cimma nasara.

Matakin ya hada dukkan jami’an tsaron Nijeriya su tabbatar duk wani kayan abinci da shinkafa kar su shigo cikin Nijeriya, masu fita da man fetur suma abin ya yi masu wahala a rufe boda da aka yi.

Jami’an gwamnati daban-daban sun nuna akwai yiwuwar sake bude bodar a watan Junairun sabuwar shekara.

Ministan ciniki da saka jari ta kasa Hajiya Maryam Katagum a zantawarta da manema labarai ta ce gwamnatin tarayya har yanzu ba ta kai ga matsayar lokacin sake bude boda ba.

Ta ce har yanzu ana kan tattaunawa da Kasar Nijar da Benin kan lamarin kafin sake bude bodar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *