Spread the love

Jam’iyar PDP mai adawa a Nijeriya ta dauri aniyar dunke barakar dake cikin jam’iyar da kara fito da hanyoyin karfafa jam’iyar kafin su cimma matsayar yankin da zai tsayar da dan takara a zaben gaba na 2023.

A zaben 2019 da ya gabata jam’iyar ta tsayar da dan Arewa wanda ya sha kaye abin da ya haifar da cece-ku-ce a tsakanin bangaren Kudu da Arewacin Nijeriya.

Wani jigo a jam’iyar ya ce suna son su kaucewa duk wata rigima dake iya tasowa a yanzu kan maganar bangaren da zai fitar da dan takarar shugaban kasa.

Ya ce suna da bukatar sai duk sun hada kan tsoffin ‘yan takarar shugaban kasarsu wuri daya, suna da bukatar lokaci kafin sanin in da za su tura takarar, haka kuma akwai rigimar ta bambancin ra’ayi da bukata.

Sakataren yada labarai na jam’iyar Kola Ologbondiyan ya ce suna da bukatar sai sun karfafa jam’iyarsu da dawo da ita cikin hayacinta kafin yin maganar yankin da zai fitar da dan takarar shugaban kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *