Gwamnatin tarayya ta fitar da jerin sunayen mutane dubu goma sha tara da dari biyu da saba’in da uku da suka fadi jarabawar kwarewa ta malanta ta kasa wadda majalisar malamai ta kasa ta shirya(TRCN) domin fitar da kwararrin malamai a kasa.

Magatakardan hukumar Farfesa Segun Ajiboye ne ya sanar da hakan a lokacin zantawarsa da manema labarai a Ibadan.

Ya ce mutum dubu 53 da 674 suka tsallake tantancewar.

Gaba daya sakamakon da aka fitar ya nuna mutum dubu 72,947 suka rubuta jarabawa a cibiyoyin jarabawa daban-daban na kasar Nijeriya daga cikinsu ne sama da dubu 19 suka sha kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *