Spread the love

‘Yan majalisar waƙillan Nijeriya sun amince da ƙudirin dawo da Tolget da soke hukumar da ke gyaran manyan titunan ƙasa FERMA.

Kan haka za a fara biyan harajin amfani da hanyoyi ga ababen hawa gaba ɗaya.

Wannan ƙudirin da aka amince da shi an kawo shi tun a majalisa ta 8 amma wannan ce ta amince da shi.

Dokar ta bayyana motocin jigila da ake sufari da su da waɗan da aka shigo da su daga ƙasashen waje za su riƙa biyan haraji na 0.5.

A duk sanda aka shigo da mota a wajen ƙasa akwai lasin ko wasu kiɗin ƙasa za a biya kashi 10 kafin mallakar lasin.

A 2007 aka yi gyaran fuska ga doka aka baiwa FERMA damar karɓar kashi biyar ga kudin man fetur da Dizel su kula ds manyan hanyoyin ƙasa a kudin kashi 40 su kula dana ƙasa, kashi 60 su kula da hanyoyin jihohi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *