SULHU NE MAFI AMFANI A DAMBARWAR NAN TA SIYASA A ZAMFARA

Na saurari audio na bayanin da abokina Honarabul Jamilu Zannah yayi dangane da hujjojinsa na aje mukamin Kwamshinan Ilmi da aka nada shi bayan dawowa daga Indiya.

Hakika a nasa ra’ayi naga yana da hujjoji masu karfi akan wasu daga cikin batutuwa; sai dai bai dace ya baiyana su kai tsaye ga yadda yayi ba.

Ina ganin muhimmin abin da ya dace abashi shawara, mussaman ga irina da ya san sirrin abin da yake faruwa a jihar Zamfara, ina baiwa yan uwana Zamfarawa da su yi wa juna uzuri da sirrinta matsalolin cikin gida akan lamuransa ko daukar wani mataki.

Wannan matsalar ana iya sulhuntawa tsakaninsu a tare da niyyar samun mafita ba tare da fitowa fili ana fallasa juna ba, a matsayin uwa daya uba daya.

Tun da akwai hanyoyin gyara anan gaba yana da kyau Gwamna Mutawalle Maradun da ya hana mayar da martani akan DG Campaign dinsa, ya nemi Jamilu Zannah su zauna tsakaninsu don warware matsalolin da yake ganin bai dace ayi su ba.

Gwamnatin Zamfara idan ana zancen gaskiya ba ta yan PDP kadai bace; don kuwa baki daya mutanen Zamfara sun aje siyasa gefe daya suka yi mata fatan alheri da tabbatuwar ta lokacin da kotun Koli ta yi fatali da zaben APC.

Kowane dan Zamfara ya cancanci rike ko zama a bisa kowane mukami don bayar da irin gudumuwar da dace ga ci gabanta da zaman lafiya da inganta tsaro.

Ina bayar da shawara ga dattawan jihar da su tsoma baki don ganin an warware wannan matsalar ta fahimta da aminci da juna.

Lokaci irin yanzu na bukatar hakuri, aiki tukuru da zaman lumana tsakani don ganin an tabbatar da muhimmin kalubalen da gwamna Mutawallen Maradun ya mayar da hankali na gyara da inganta rayuwar al’ummar jihar baki daya.

Idan har jihar Zamfara akayi mata mugun data ko kyale ta shiga wani rikicin siyasa ko dauke hankalinta ga sha’anin tsaro da kwanciyar hankali, hakika jihohin dake makwabtaka da ita zasu fuskanci matsalolin, mussaman akan lamarin tsaro da hayaniyar siyasa.

Ra’ayi ne daga wani ɗan jihar Zamfara da bai buƙaci a bayyana sunansa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *