Spread the love

Rukayya Umar Santa wadda aka fi sani da Dawaiyya sananna ce a masana’antar shirya finafinnan Hausa ta yi magana kan dalilinta na shiga harkar siyasa.

Ta ce ba wani abin wahala ne dan wasan Hausa ya shiga siyasa ba.

“Ina da yakinin cewa siyasa na tafiya tare da shahara mu sanannu ne, ka ga ba wani abin wahala anan. Hakan dai yana iya sanya ni cikin siyasar gadangadan”

“Na tsunduma cikin siyasa sosai na yi wa kamfen ganin samun nasarar shugaban kasa Buhari da Gwamnan Kano Ganduje da Katsina Masari, na yi farincikin nasarar da muka samu.” in ji Dawayya.

Ta yi magana kan wasu mutane na ganin a matsayin maras tarbiya ta ce ‘lokaci ya yi da yakamata mutane su rika kallonmu a matsayin mutane irinsu diyasu muke, su fahimtar da mu kan kuskurenmu, wasan Hausa sana’a ce kamar kowace, bai kamata ana yanke mana hukunci ba kan kuskuren mutum daya, wannan abun ya dade ana yi ba a daina ba, sai dai ina farainciki yanda aka fara bambance abin da muke yi da kuma abin wasu da ba mu ba ke yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *