Spread the love

Ministan shari’a babban lauyan gwamnatin tarayya Abubakar Malami ya fitar da bayanin cewa tsoffin gwamnoni 22 ne suke bincike kan zargin wawushe kuɗin jama’a.

Ya yi wannan bayanin ne a zantawarsa da manema labarai a Abuja, Malami ya bayyana yaƙi da rashawa na shugaba Buhari amatsayin wanda aka mayar da hankali gaba ɗaya ba tare da nuna bambancin ƙabila ko jam’iya ba.

Minista haka ma ya bayyana da yawaan sanatoci masu ci suna cikin binciken na gwamnatin tarayya, rashawa ba ta da kaɗan tana gurgunta tattalin arziki da cigaban jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *