Spread the love

Daga Datti Assalafiy

Maigirma shugaban Kasarmu Nigeria Muhammadu Buhari ya ziyarci babbar hedikwatar rundinar ‘yan sandan Nigeria (Lois Edet House Abuja) inda ya kaddamar da sabbin motocin yaki na ‘yan sanda da dakunan tattara bayanan sirri wanda aka yiwa take da:
-National Police Crime and Incident Database Centre (NPC & IDB)
-Nigeria Police Force National Command and Control Centre (NPF-C4i)
da sauran sabbin kayan aikin ‘yan sanda.

Maigirma shugaban kasa Buhari yayi alkawarin cewa zai inganta aikin ‘yan sandan Nigeria tun daga bangaren bayar da horo, kayan aiki da lura da walwala da jin dadinsu, domin suyi aiki yadda ya dace da doka da cigaban zamani.

“..Don cimma wannan buri, shiyasa na karawa ‘yan sanda albashi, sannan na bada umarni a dinga diban sabbin ‘yan sanda dubu 10 a duk shekara, saboda a karawa ‘yan sandan karfi da yawan jami’ai a magance matsalolin tsaron cikin gida..”, inji shugaba Buhari.

A karshen jawabinsa, Maigirma shugaban kasa Buhari ya yabawa jagorancin Maigirma babban sufeta janar na ‘yan sandan Nigeria IGP Muhammad Abubakar Adamu bisa yadda ya kawo sauyi mai ma’ana a rundinar ‘yan sandan Nigeria, da kuma tabbatar da tsaron cikin gida, duk da ya karbi jagorancin rundinar ‘yan sandan a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalolin tsaro kamar garkuwa da mutane, fashi da makami, matsalar ‘yan bindiga da sauran miyagun laifuka.

A nasu jawabin, Maigirma shugaban rundinar ‘yan sandan Kasarmu Nigeria IGP Muhammad Abubakar Adamu, da Maigirma Ministan ‘yan sandan Nigeria Maigari Dingyadi sun yabawa shugaba Buhari bisa cikakken goyon baya da yake baiwa rundinar ‘yan sandan Nigeria.

yanzu kayan aiki da na’urori na leken asiri da tattara bayanan sirrin tsaro da bin diddigi sun fara samuwa, ‘yan ta’adda da maciya amanar tsaron Nigeria kun shiga uku.

Muna rokon Allah Ya taimaki rundinar ‘yan sandan Nigeria da shugabanninta da Maigirma shugaban kasa, Ya basu ikon magance mana dukkan matsalolin tsaron Kasarmu Nigeria koda azzalumai da makiya da ‘yan kwangilar ta’addanci basa so

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *