Spread the love

Mutum dubu biyu da dari bakwai da arba’in da biyar ke jiran a zartar musu da hukuncin kisa ne ke zaune a gidajen yari dake fadin Nijeriya gaba daya.

Darakta Janar na hukumar gyaran halaye ta kasa Jafaru Ahmed ne ya bayyana haka a zantawar da manema labarai a rangwadinsa da yake wata cibiya a Gwagwalada cikin birnin Abuja.

Ahmed a tabakin wakilinsa mai magana da yawunsa Francis Enobore ya ce rashin sanya hannu da wasu gwamnoni ke yi ga wadan da aka yanke wa hukuncin kisa yana daga cikin abin da ya kawo cikinkoso a gidajen yari.

Ya ce wasu gwamnoni ba su son sanya hannun a zartar kisa ga wadanda aka yanke wa hukuncin kisa ko wanda zai kare rayuwarsa gidan yari da ake kira ‘Condemned’

Ya ce an yi yawa hakan ya sa wasu ba su karbar mutane in an kaisu koyon sana’a don gudun cunkushewarsu.

Ya ce akwai wasu tsoffin mambobin Boko haram da suka canja halinsu har sun yi jarabawar kare makarantar Sikandare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *