Shirin da gwamnatin tarayya take da shi na gyaran zauren majalisun tarayya da ofishoshinsu domin samar da yanayi mai kyau a wurin.

Kudin a saka su kasafin kudin shekara mai kamawa na tiriliyan 10.594, wanda shugaba Buhari ya sanyawa hannu a ranar Talata data gabata.

A bayanin da aka samu an gina kafaren wurin a shekarar 1999, in da ya lakume dala miliyan 35.18 kudin Nijeriya biliyan 10.7 kenan kudin da aka ware na gyaran wurin a yanzu sun nunka wanda aka kashe a gina wurin sau uku a shekara 20 da suka gabata.

Mafiyawan ‘yan kasa masana tattalin arziki da masu kare hakkin dan adam da ‘yan kasuwa da talakawa sun bayyana kashe wadan nan kudi ga yin wannan gyaran ba shi ne abin da yafi kamata abaiwa muhimmanci ba.

Kudin suna iya gina karamar asibitin yanki dubu 27, a tsarin cigaban lafiya na duniya a cikin kasashe 191 da harkar lafiyarsu ke ci baya Nijeriya ce ta 187. Miliyan 10 suna iya gina karamar asibiti da duk duniya za ta aminta da ita a sanya kayan aiki cikinta da magani da kwararrun ma’aikata.

Kudin sun isa su gina ajujuwan daliban karatu guda dubu 10,360, in aka gina Bulok 2,590 mai ajujuwa hudu a duk Nijeriya kowane kan kudi miliyan 13.5, in aka sanya kudin ga wannanhaujin a makarantun Firamare da kananan sikandare za a iya samun wannan adadin ajujuwan, zai samar da gibin da ake da shi da kusan 4.5, a kasar gaba daya ana bukatar ajujuwan dubu 222,426.

Kudin suna iya gina gida mai dakuna guda biyu guda 12, 333, in kowane gida za a gina shi kan miliyan uku ga kudin suna iya samar da gidaje masu saukin kudin a Nijeriya abin zai rage karancin gidaje da ake da su, a Nijeriya ana bukatar gidaje miliyan 17.

Bayan nan kuma suna iya gina gida wanda ya karba sunansa gida 2,055 a kowane yankin a cikin yankunan Nijeriya shidda da ake da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *