Spread the love

Ma’aikata da masu karbar fansho a jihar Borno sun fara karbar hakkinsu a umarnin da gwamna Babagana Umara Zulum ya bayar kar a bari a kai ranar Laraba ta kirisimeti kowane ma’aikaci da mai karbar Fansho bai karbi kudinsa ba.

Gwamnan ya ba da umarnin ne ta hannun mai magana da yawunsa Malam Isa Gusau, an yi hakan ne domin kirstoci su shiryawa bukinsu cikin lokaci.

A jawabin da ya fitar a ranar Laraba data gabata ya ce biyan albashin yana cikin rashin wasa da hakkin ma’aikata da gwamna ke yi hakan ya sanya ba a rike kowa kudi ba.

Ya ce gwamna Zulum kowane lokaci baya kallon biyan albashi a matsayin wata nasara ta gwamnati domin bashi ne ka biya da ya rataya kan wuyan gwamnati bisa ga tsarin doka, kamar yadda ake tafiyar da gwamnati dan kwangila ne da mai aikin. Hakan yasanya ba wasa da biyan ma’aikatan Borno duk wata suna karbar albashin daga ranar 26 ba a fasa ba kuma, kan wannan al’adar ce ya sa Zulum ya biya albashhin watan Disamba nan take.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *