Shugaban hukumar Zakka da wakafi ta jihar Sokoto Malam Muhammad Lawal Maidoki ya nuna farincikinsa ga nasarar da hukumar ta samu na daukar nayin maganin masu lalurar tabin hankali guda 32 da aka kamo a sassan jihar ganin kwalliya na biyan kudin sabulu.

Malam Muhammad Maidoki ya nuna hakan ne a wurin rabon kudin magani miliyan shidda da rabi na wata-wata da gwamnatin Sokoto ke bayarwa ta hannun hukumar ta rabawa a dakunan maganin da suke hulda da su don amfanin mabukatan jihar, ya ce masu tabin hankalin 32 da hukumar ta kai asibitin gwamnatin tarayya ta masu lalutar kwakwalwa dake garin Kware wasu daga cikinsu sun samu lafiya.

“Duk da akwai dan kalubale a cikin wadan da suka samu lafiyar akwai kurma cikinsu ba mu san danginsa ba, kuma shi bai san in da suke ba, muna kan kokarinmu mu ga yanda za mu yi don sanin in da kurman ya fito tun da ya samu lafiya a yanzu” in ji Maidoki

Ya yi kira ga jama’a musamman wadanda ke da masu tabin hankalin gidajensu da su yi hobbasar kai ‘yan uwansu asibitin, dubu 48 ne ake karba a sati hudu, ba wai su rungumi hannuwa suna kallonsu ba, hukumar Zakka ba ta iya game ko’ina marasa karfi da marayu tafi mayar da hankali kansu.

Maidoki ya nuna gamsuwarsa yanda aikin tattara bayanai na asusun kiyon lafiya ke tafiya a gundumar Tudun wada a karamar hukumar Sokoto ta kudu ke tafiya.

One thought on “Masu tabin hankali 32 da hukumar Zakka da wakafi ta dauki nauyin maganinsu suna samun sauki”
  1. Hi. I have checked your managarciya.com and i see you’ve got some duplicate content so probably it is the reason that
    you don’t rank hi in google. But you can fix this issue fast.

    There is a tool that generates articles like human, just search in google: miftolo’s tools

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *