Spread the love

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa yankin a jihar Sokoto ta damka babur mai kafa uku waton adaidaita sahu ga gwamnatin Zamgara.

Babur din guda 53 hukumar ta kwato shi ne ta mikawa gwamnatin Zamfara domin nasu ne.

Shugaban hukumar Abdullahi Lawal ne ya mika baburan hannun Sakataren gwamnatin jihar Zamfara a ofishin hukumar dake birnin jihar Sokoto.

Shugaban ya ce a halin yanzu hukumarsu na binciken sama da abubuwa daban daban sama da 60 a jihar Zamfara da suka shafi daidaikun mutane da gwamnati da wasu hukumomi masu zaman kansu, da yawan kudinsu za su kai sama da biliyan 200, akwai da yawan asusun ajiya na banki da hukumar EFCC ta rufe saboda bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *