Yanzu babbar tambayar da muke da ita shi ne ya dace mutum ya yi komai saboda so duk ko yanda abin yake da wahala ko cutarwa za ka yi domin wanda ka ke so?

Da yawan mata suna gwada masoyinsu da cewa duk abin da suka sa shi yana yi saboda su. A dangantaka da yawa mutum na barin wani abu domin saboda samun zaman lafiya da zamantakewar da ke tsakanin juna. In muna cikin kogin soyayya da yawan burin da ake da shi bai fiye cika ba sai ka ga an dawo ana wasu abubuwan da a karshe za su haifar da danasani.

Wane tsawon lokaci kika dauka kina cikin kogin So da shaukin kauna, a wannan lamarin kuma sau nawa kika yi abu saboda so? Tambayar da Managarciya ta yi wa wasu mata a jihar Kebbi.

“Wannan so da ake magana kansa ya gaskiyar shi take, wani yanayi ne da kake ji tsawon watanni ko shekarru kan wani bayan wani lokaci kuma ya kode, in dai haka ne ya za ka yi komai saboda so, kawai na yi ne don ina son shi a wurina wannan ba aikin hankali ba ne, zan nuna so ga wanda nake yi wa shi amma ba zai wuce abin da nake iya wa ba” Mabaruka Muhammad

Maryam Ibrahim ta ce “In dai ina son mutum zan iya komai saboda shi zan wahalar da kaina ya tabbatar ina son shi, in har na kasa yin sadaukarwa gare shi ya zai tabbata ina son shi da gaske, kar ka mance fa kashe kai ne kawai zai faranta ran masoyi ka samu son shi a hannunka. Sadaukarwa fa yakamata ta zama cikin jinin mutum masoyi ba wai wani abu ba ne sabo, duk macen da ba ta nuna so ga namiji dole a karshe ya barta don ya gane ba son shi a wurinta.

Asabe Hussain ta ce So kalma ce kawai tsakanin juna ba wani abu da yake iya bayyana so a zahiri saboda ba wani abu ne da ke wanzuwa ba.

A ganinta kenan ba So ita tana ganin kalma ce kawai in ka ce akwai so ya yake mi ya sa yake gushewa ko cin zarafin masoyi a cin amanarsa kila ma da akwai kalmar so sai dai a ce Son kai, amma ba wai wannan soyayyar mai cike da yaudara da zalunci ba.

Ta ce akwai lokacin da ta taba gwada kalmar ta so ta sadaukar da komai nata ga son a karshe dai ta gane bata lokaci ne kawai ta samu, kan haka tabar yin komai da sunan SO.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *