Spread the love

Dan asalin jihar Sokoto mai kishin matasa da jiharsa Injiniya Zayyanu Tambari Yabo ya shirya taron fadakarwa a karo na biyu domin duba makamashi ga cigaban kasa.

Wannan taron fadakarwar da ya gudana a Otal din Giginya a Assabar data gabata shi ne irinsa na farko da ake samu mutum guda a Sokoto ya shirya a kashin kansa domin kawai samar da fahimta da ilmi ga mutanensa.

A wurin taron Injiniya ya yi magana ga mahalarta taron ya ce ‘Muna godiya ga mahalarta taron karo na biyu yanda suka karba gayyatar nan abin ya kara min karfin guiwa, ga wannan kudiri nawa.

“Mun fito da wannan tunani ne domin mu baiwa al’umma dama su samu wata kafa ta tattaunawa da masana domin cigaban jama’armu game da lamurran yau da kullum, daular Usmaniya an kafa ta ne kan ilmi dole ne mu cigaba asassa asalin don cigaban jihar mu, kamar yadda muka yi na gayyato masana aka tattauna kan makamashi da cigaban kasa, haka za mu ci gaba da tattaunawa kan cigaban al’umarmu har a samu nasara” a Cewar Injiniya Zayyanu.

A karshen tattaunawar an fahimci wasu lamurra da yawa gefen makamashi da ba su kamata a rika wasa da su ba a gefen gwamnati da jama’a da suka kunshi ganewar makamashi yana da matukar muhimmanci ga rayuwar mutum, akwai bukatar matasa su shiga harkar bunkasa makamashi don ba da ta su gudunmuwa, da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *