Spread the love

Sanata Iya Abubakar Dakta na farko a duk arewacin Nijeriya, ya samu Farfesa a fannin lissafi yana dan shekara 28, ya wakilci al’ummarsa a majalisar dattijai karo biyu yau ya cika shekara 84 da haihuwa.

Ya kammala karatunsa na digiri na uku a jami’ar Cambridge, bayan kammala digirinsa na farko a jami’ar Ibadan a mataki na farko waton first class a fannin Lissafi, da shekara 38 ya zama shugaban jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, ya yi karantarwa a jami’ar Michigan a USA da jami’ar City a New York .

Iya Abubakar dan kwanya ne da ya ba da gudunmuwarsa a cigaban gwamnati ya yi zama darakta na farko a bankin kasa CBN, ya zama ministan tsaro da ministan cikin gida a lokacin mulkin Shagari.

Dan jihar Adamawa ne ya yi Sanatan Adamawa ta Arewa har karo biyu daga baya ya yanke shawarar ba zai sake takara ba.

A lokacin da ya yanke shawara daina tsayawa takara manema labarai sun tambaye sa dalilin yin haka ya ce akwai mutanen da suka dace su nemi kujerar ba dole sai shi kadai ba. Da yawan Sanatoci ba su ji dadin haka ba ganin yanda yake cikin masu ilmin kasar nan ba wai majalisa kawai ba domin ana karuwa da gudunmuwarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *