Spread the love

A shekarar 2014 watan Disamba 9 masana’antar shirya finafinnan Hausa ta yi rashin shahararren dan wasan barkwanci Rabilu Musa wanda aka fi sani da Ibro.

Tun sanda aka rasa shi a masana’antar aka kasa samun madadinsa, abin da wasu mutane ke ganin da wuya a cike gibin da margayin ya bari, wasu na ganin kuma lokaci ne kawai bai zo ba za a iya samun wanda zai tashi ya yi nasa tashen shi ma kamar margayin.

Margayi Ibro yana da basira da yake juye komai ya koma ban dariya, abin da ya sanya ake girmama shi sosai a bangarensu har ana kiransa da Ciyaman, ya shirya finafinnai da yawa na shi da suka fara a Dandamali ko dabe da sunan IBRO bayan rasu wannan sunan ya mutu shi ma a harkar wasan barkwanci.

Yanzu shekara biyar da rasuwarsa da yawan ‘yan wasan barkwanci na son maye gurbinsa a masana’antar Kannywood suna iyakar kokrinsu wasu kuwa sun yi kwancinsu domin suna ganin baiwar ta shi ce kuma ya tafi da ita.

Nakan gaba cikin wadan da ake ganin suna son haye kujerar margayi Suleiman Bosho a lokacin rayuwar Ibro sun yi finafinnai tare da dama kan haka wasu masoya na ganin Bosho zai iya cike gurbin, in da wasu ke ganin margayi da kansa kamar ya nuna Bosho zai iya maye madadinsa.

Falalu Dorayi mai shiryawa da ba da umarni a Kannywood ya ce gurbin da margayi ya bari babu mai iya cika shi basirarsa da baiwarsa Allah ne ya ba shi ba a iya cike ta gudunmuwarsa da ya bayar a harkar ta daban ce.

Mustafa Naburaska da Musa Mai Sana’a sun ce da wuya a samu madadin margayi Ibro a harkar barkwanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *