Spread the love

Sanannar ‘yar wasan Hausa Rahama Sadau ta bude gidan kwalliya a jihar Kaduna.

Rahama ta bude masana’antar ne a wajen bukin cikarta shekara 26 da haihuwa a ranar Assabar data gabata.

A wurin da ta bude mai suna ‘Sadau Home’ za a rika shan Shisha abin da ya jawo hankalin mutane musamman a Arewa.

A wannan zamani da ake ciki da yawan wasu matasa sun dauki shan tabar shisha a matsayin wayewa, abin da mafiyawan masu hankalin cikin al’umma suka dauka shan wannan abar rashin tarbiya ne da jefa kai cikin hadarin shaye-shayen miyagun kwayoyi, da yawan uwayen da suka san abin da suke yi ba za su lamunce yaransu ga shiga wannan sabgar ba. Bai kamata gwamnati ta yi wasa lamarin ba gudun ka da ya je in da ba za a iya tarbo shi ba.

Da yawan mutane sun soki Rahama ga shiga wannan sana’a domin ana ganin bai dace da diyar tarbiya mai rike al’adunta na uwaye ba.

Bude wurin kwalliya ba laifi ne ga ‘ya mace ba, bayan Rahama wasu ‘yan fim sun fara karkata ga yin sana’a kamar Ali Nuhu, Maryam Yahaya, Sani Danja, wasu kuma sun kafa kungiyoyin sa-kai .

Kabiru Muhammad ya ce ‘na dade da fahimtar Rahama ba ruwanta da auna abin da za ta yi in dai ita ta gamsu da shi wanda hakan hatsari ne ga mutum. Ya za ta bude wurin shan taba ga samari don ita wurinta wayewa ne ba tare da ta kula al’ummar da take ciki ba, hakan bai dace ba’ a cewarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *