Spread the love

Sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce rashin bin umarnin kotu abu ne na gurgunta doka, ya gargaɗi shugabannin da ke ƙin bin umarnin kotu suna iya kawo rashin zaman lafiya.

Ya yi waɗan nan kalamai a Abuja a wurin taron zango na majalisar addinai ta Nijeriya. Ya ce saboda gujewa abin da zai je ya dawo, yakamata a riƙa girmama doka.

Ya ce in aka kai maka takardar umarni daga kotu dagangan ka ƙi bin umarnin kotu don kawai kana gwamna ko shugaban ƙasa ko kana da wani babban muƙami kana shirya abu ne na rashin zaman lafiya.

Ya ce ba al’ummar da za ta tafi da rashin bin doka, ‘yan ƙasa dole su cigaba da bin doka domin samun cigaban da ake buƙata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *