Spread the love

Hukumar kiyaye haɗurra ta jihar Bauchi ta tabbatar da ƙonewar mutum 28 kuma sun rasa ransu a hatdarin mota da ya faru a ƙauyen Gubi Gari dake saman babbar hanyar Bauchi zuwa Kano.

Jaridar Punch ta kalato bayanin ɗan uwan mamatan Abdullahi Yamadi bayan tabbatar da lamarin ya nuna matuƙar ɓacin ransa.

Yamadi ya ce margayan dukansu ‘yan uwan juna ne, za su tafi ziyara ne domin lokacin kaka da aka cire amfanin gona ana samun irin wannan ziyara.

Ya ce sun bar Dutsinma a Katsina sun bar Jigawa suna tsakanin Bauchi ne motarsu ta sha wata mota su 29 ke cikin motar nan dukansu sun rasu, bayan direba shi kan ya tsira, wannan abin ɓaƙin ciki ne da sosa zuciya mutum 28 ‘yan gida guda su rasu a rana ɗaya a hatsarin mota ba daɗi. A cewarsa.

Kwamandan hukumar kiyaye haɗurra ta Bauchi Abdurrazaƙ Najume ya bayyanawa manema labarai hatsarin ya faru da tsakar daren ranar Laraba in da bus j5 da huma suka gogi junansu.

Hakan ya faru ta sanadiyar mai huma ta ƙwace masa ya sha mai j5.

An ɗauki gawawarkin da suka ƙone da direban da ya tsira an kaisu asibitin koyarwa ta Abubakar Tafawaɓalewa.

Da safen yau Jumu’a an yi wa mutanen salla an biznesu kamar yadda shari’ar musulunci ta tanadar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *