Wani Ɗan Nageriya (Madandatsin Yanar gizo) da ake Kira da Mai basira marar misaltuwa Mai suna Abaeze Atuche Ya yi abin da ya bawa kowa mamaki Wanda ya sa shi shiga komar hukuma.

Ya samu yin kutse ne a yanar gizon masu kula da shige da ficen ƙasar Amerika (wato Immigration).

Abaeze Atuche ya samu sa’ar baiwa dukkan ‘yan uwansa da mutum goma sha biyar(15) daga cikin abokanansa takardar zama ta din din din a Amerika.

Har yanzu Jami’an Shige da ficen ba su gano hanyar da ya bi ya yi wannan kutsen ba, sai dai ma an gano Cewar, a Shekarar 2013 Abaeze ya shiga Amerika da takardun bugi, ba tare da an gano shi ba.

Jamilu Sani Rarah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *