Spread the love

Jam’iyar PDP mai adawa a Nijeriya ta bayyana kalmomin Uwar gidan Shugaban ƙasa Aisha Buhari magana ce ta ɓacin rai da ke nuna kasawar gwamnati da ya sanya rashin kataɓus ga jagorancin Muhammadu Buhari.

Bayanin da jam’iyar ta fitar ta hannun sakatsren yaɗa labaranta Kola Ologbodiyan ya ce wannnan lamari ya fito da kasawar gwamnatin Buhari a wurin cimma nasarar cigaban ƙasa.

PDP ta ce bayanin Aisha ya bayyana akwai wani mutum a fadar shugaban ƙasa da ke zartar da lamari ba tare da sanin Buhari ba, abin da ke nuna a zagaye yake da ‘cabal’

Jam’iyar ta yi kira ga Buhari da ya daidaita gidansa, ya kuma tseratar da ƙasa ga abin kunya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *