Spread the love

HOTONN KI ABIN SONKI ABIN QINKI: KO DON MUTUWA KYA ZABI NA GARI KI DAURA A PROFILE
‘yar uwa ina baki shawara da ki san irin hotunan da zaki rika sawa a #SocialMedia ko dan tsaron Allah ko kuma dan tsoron sharri da kage gare ku.
Gaskiyar magana ba karamin matsala ba ne mace ta dauki hotonta ko domin ta nuna kanta ko kuma ta saka shi a profile domin jama’a su gani.
Mafi yawan hotunan da ake sakawa a cikin dandali da ake nuna mace cewar ina bukatar miji ko ina bukatar wanda zai gamsar da ni ƙarya ce tsagwaronta ake yi musu.
‘Yar uwa daure ki cire hotunanki kakaf a cikin irin wadannan shafuka domin akwai mutanen da ba su da mutunci ba su da tsoron #Allah, suna daukar hotunanku suna yin ƙarya iri-iri da ɓata muku suna.
Nasan kina jin daɗi idan kika saka hoto aka yaba, ko ace kinyi kyau, wasu su ce kin haɗu, amma ki sani ranki zai ɓaci ko na ‘yan uwanki ko na yayanki idan suka ga an ce kin rasa mijin aure ko kina bukatar namiji domin biyan bukatarki.
Kuma baki san wani abu ba da zarar an sanar da rasuwar wani abin da ake yi sai kawai a tsallaka profile din shi a dauko hotonsa ana neman mishi gafarar Allah.
Na ga mata da yawa da aka saka hotunansu bayan sun mutu babu koda gyale a jikinsu ballantana hijabi, musan rabin kirjinsu a waje ga su da shiga da Allah ke fushi da ita kuma wai ana nema mata gafara.
Duk da cewar maza da dama suna daukar hotunan ku su ajiye a cikin wayoyinsu da zarar kun saka a social media, kuma wasu suna tara irin wannan hotunan domin bata muku suna sai dai har yanzu lokaci bai bace ba, je ki cire su.
Zaki iya zama a social media ba tare da saka hotonki ba, ki saka wata flower ko wani abu da zai zauna a matsayinki ba wai ainihin hotonki ba. Ki sani duk mazan da suke cewa kin yi kyau ko kin hadu, domin kin fito da rabin kirjinki, ko gashin kanki, ko kin matse jikinki lokacin daukar hoton, Allah kashi 90% cikinsu ba za su yarda ki zama uwar ‘ya’yansu ba, da kuma za su bayar da misalin mace ta banza hotonki shi ne abin misalinsu.
Ku kuma samari da ba ku ji dadin wannan maganar ba, ku yi hakuri kuma ku kwatanta irin wannan al’amari ga matar da zaka aura ko yarka ko kanwarka.
Duk da mutumin kirki ya ke iya ganin abin kiri, mutum banza abin banza ya ke gani a matsayin abin kirki.
Ba dole nasiha ce kawai!!!

Shafiu Garba
Sashen kula Da kafafen sadarwa na
MANAGARCIYA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *