Spread the love

Uwargidan Shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari ta zargi mataimakawa Shugaban kasa kan kafafen yada labarai, Malam Garba Shehu, da karkata biyayyarsa ga wasu mutane daban da ke cikin wannan gwamnati yabar Shugaba Buhari.

Uwar gidan Shugaban kasar ta zargi Malam Shehu ne da laifin kin kare iyalin shugaban kasar, amma ta yi zargin cewa ya zabi yakar ta ne ta hanyar “kafafen yada labarai na zamani” don bata suna da ‘ya’yanta.

A cikin wata sanarwa da ta sanya wa hannu, a safiyar ranar Laraba mai taken ” Garba Shehu ya fara wuce gona da iri ” ta ce, ” Babban abin da Garba Shehu ke yi shi ne yaɗa jita-jita akan ta a kafafen Social Media domin ya bata mata suna da ‘ya’yanta.

Ta ƙara da cewa babu wata yadda da ta rage tsakanin iyalin shugaban kasa da Garba Shehu a halin yanzu tunda ya kasa tsayawa tare da yin biyayya ga mutum daya ko guri daya.

“Don kara tabarbarewa, Garba Shehu ya gabatar da kansa ga wadannan mutane a matsayin wanda zai iya aiwatar da manufofinsu a gwamnati har ma ga matakin tsoma baki cikin al’amuran iyalin shugaban kasa. Wannan bai kamata ya ba”.

Ta ce ta karaya da Malam Shehu ne tun lokacin da bidiyon ta da Fatima Mamman Daura ya yadu a Social Media amma Garba Shehu a matsayinsa na wanda ya san gaskiyan abin da ya faru ya kasa cewa ko yin komai.

“Garba Shehu a matsayin sa na Kakakin fadar shugaban kasa ya san gaskiya kuma yana da alhakin shirya bayanan kai tsaye game da abin da ya shafi iyalin shugaban kasa ko shi kanshi shugaban kasa, amma saboda biyayyarsa na ga wasu daban wadanda ba su dace ba, da gangan ya ki cewa duniya komai wanda sakamakon haka ne ya rushewa dukkan aminci da yarda dake tsakanin iyali na da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *