Spread the love

Sarakunan Arewa sun yi taro a Kaduna sun tattauna kan matsalolin da ke fuskantar yankin Arewa da ƙasa baki ɗaya.

Shugaban majalisar sarskunan Arewa Sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar kalamansa wurin taron ya ce wanzuwar Nijeriya suka sanya a gaba.

Haka ma ya baiwa gwamnatoci a dukkan mataki tabbacin sarakuna ‘yan uwansu ne a haujin cigaba, kan haka za su cigaba da baiwa gwamnati shawara kan abin da za ta yi kuma yana da tabbacin za su saurare su.

Ya ce za su cigaba da kwaɓar shugabannin siyasa a in da hakan ke buƙata za su ci gaba da ba su shawarar su ji tsoron Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *