Spread the love

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya umarci babban akawun gwamnatin tarayya ya riƙa buga bayanan kuɗin da gwamnati ke kashewa kullum.

Kullum za a samu bayanin kuɗin a wannan adireshi www.opentreasury.gov.ng turaka ce da aka buɗe da za ta ɗauki shige da ficen gwamnati na sama da miliyan biyar(5m).

Buhari ya ce bayanin zai ƙunshi abin da ya shigo da wanda ya fita a kowace rana.

Ya ce kowace ma’aikata da hukuma ta gwamnatin tarayya su riƙa sanya bayanansu ba tare da kasawa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *