Home Ra'ayi Asalin Sanata Wamakko da kalmarsa da ya kira Bafarawa 'Ɗan ci-rani'

Asalin Sanata Wamakko da kalmarsa da ya kira Bafarawa ‘Ɗan ci-rani’

Martani; ASALIN SANATA ALIYU MAGATAKARDA WAMAKKO A JAHAR SAKKWATO DA KUMA TABBATAR BAFARAWA ” DAN CI RANI ” A SAKKWATO.
Rubutawa.
Hakika jama’ar jihar Sakkwato a jiya Litinin sun kwana cikin wata sabuwar danbarwa siyasa wadda take yawo a yanzu haka, kan wasu maganganun na tsohon gwamnan Sokoto Attahiru Dalhatu Bafarawa wanda tuni Dattijon Arziki Sanata Aliyu Wamakko ya riga ya masa ritaya a ɓangaren siyasar Najeriya. Maganganun na Bafarawa akan Sanata Wamakko suka jawo cigaba da tsinuwa tare da Allah wadai akan shi daga mutane daban daban na Sakkwato wanda da yawa suke cewar ga alamu Bafarawa ya giɗime ne kan batun shari’arsa ta kuɗin makamai

Duk wani wanda yasan halayen Bafarawa, kuma yasan tabbataccen asalinsa, kana kuma yasan asalin tarihin Kakanninsa da inda ya fito, to ba zaiyi mamaki fitowar irin wadannan kalamai ba daga bakin Bafarawa ba, hakazalika dukkan alamu sun nuna cewar koda Bafarawa yake wadannan kalamai akan Sanata Wamakko a filin jirgi yana cikin rashin kwanciyar hankali tare da tsoron zai je Abuja wajen shari’ar kudin makamai da hukumar EFCC ta sanyasu kara shi da dansa Sagiru, wadda Bafarawa da idonsa ya sheda kuma yagani a zahiri a satin da ya gabata karara wata kotu ta yankewa tsohon Gwamnan Abia shekaru 12 a gidan yari saboda almundahana da kudaden al’umma irin yanda ake zargin Bafarawa ya aikata da kudaden makamai, don haka Bafarawa yana ganin tamkar tafiyar da yake kai ba me dawowa ba ce sai gidan yari. Shi yasa yayi amfani da wannan dama a cikin irin nasa ya gayawa Sanata Wamakko wadannan maganganu na rashin dattako. Amma Hausawa na cewa idan kasan abunda zaka fada, to tabbas baka san abunda za’a mayarma ka ba.

A wannan rubutu na martani da na rubuta zamu yi duba ne tare da tsokaci akan waye yake da cikakken asali a jahar Sakkwato tsakanin Dattijon Arziki kuma Jagoran siyasar Jahar Sakkwato da Arewa baki ɗaya da Attahiru Bafarawa.

A bangaren Sanata Aliyu Wamakko :

Shi dai Sanata Wamakko cikakken sunansa shine Aliyu Magatakarda Wamakko kuma an haifeshi ne a ranar 1 ga watan 3 na shekarar 1953 a garin Wamakko daga tsatson mahaifinsa Margayi Barade Jabbi wanda yake rike da Sarautar Baraden Wamakko na farko a wanchan zamani.

Dukkan littafan bayanen tarihi na turawan mulkin mallakar Ingila wanda sukayi rikon yankin Sakkwato a wanchan zamani, tareda bayanai na Malamai, Sarakuna da abokane wanda sukayi zamani da Maigirma Baraden Wamakko na farko Muhammadu Jabbi kuma Mahaifin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, sun bayyana Muhammadu Barade Jabbi a matsayin Basarake me tausayin talakawansa, Dattijo me yawan kyauta, Malamin Makarantar Addini wanda yake tursasa iyalansa da sauran al’ummarsa kan neman ilimin addini dana boko a wannan zamani nasu da ake kyamar karatun boko, Ma’aikacin lafiyar dabbobi ne dake yawan duba lafiyar dabbobi a Ruga ta makiyaya da fulani, Babban Manomi ne da nomansa yake zagayo shekara, mutum ne me kiyaye martabar addininsa kuma wanda ya zurfafa wajen sanin ilimin Al-qur’ani maigirma, Hadissan Manzon Allah (SAW) da kuma ilimin iya mu’amala tareda hulda da jama’a.

Sannan Sarautar Baraden Wamakko ta mahaifin Sanata Aliyu Wamakko wato Muhammadu Barade Jabbi me asali ce da inganci har a cikin tarihin jihadin mujadddadi dan fodiyo, domin Sarkin Musulmi Abubakar ne ya nada shi a shekarar 1955 shekara biyu bayan ya samu haifuwar jinjiri kuma hazikin yaro wanda yanzu shi ne ya zama abun alfaharin Sakkwatawa da mutanen Arewa waton Sanata Wamakko wanda aka haifa a shekarar 1953.

A bangaren asali na Mahaifiya kuma, shi Mahaifin Sanata Wamakko waton Barade Jabbi yanada Mata guda hudu tun daga Hajiya Saudi da Hajiya Mowa da Hajiya Aminatu da Kuma Hajiya Aishatu Ige wadda itace mahaifiya kuma sanadi a bangaren uwa mace ga samuwar bawan Allah Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko. Mahaifiyar Sanata Wamakko Marigayi Aishatu Ige itama me cikakken asali ce a jahar Sakkwato domin ta fito ne daga kauyen Fanare na garin kammata a yankin mulkin Wamakko ta Jihar Sakkwato a halin yanzu. Margayiya Aishatu Ige ta haifi diya biyar daga cikinsu akwai mace daya da kuma maza hudu wanda Sanata Aliyu Wamakko yana daga cikin mazan hudu. Babban abun da ake yabo a mahaifiyar su Sanata Wamakko shi ne irin kyakkyawan dabi’unta da kuma halayenta tare da nasabarta da iya renon ya’yanta cikin tarbiya da kuma yawan riko da Addini. Yau kowaye koda makiyi ne ga Sanata Wamakko zai masa sheda da yawan riko da addini da kuma tawakkali ga Allah, wannan ya samo asali ne daga irin reno da ya samu ga mahaifiyarsa margayiya Aishatu Ige.

Abun alfahari da kara godiya ga Allah shi ne, Ita kanta kasar Wamakko inda asali na Sanata Wamakko ya ke ta samu asali ne daga Kakan shi Sanata Wamakko wanda ake kira Muhammadu Machunga, mashahurin barde ne a yankin Afrika kuma mayaki ne, sannan me kishin assasa daular musulunci ne a duk inda ya samu kansa wanda hakan yasa a lokacinda zai shigo garin Sakkwato don kara hada kai da Mujaddadi Shehu Usmanu Danfodiyo (Allah ya karamasa rahama) wajen kafa Daular Usmaniyya sai da ya fuskanci artabo daga mayakan kasar Gobir wanda suka masa barazanar kada ya kuskura ya zo kuma suke kiyayya da addinin musulunci saboda maguzanci da suke yi a lokacin wanda nan ne cikakken asali na shi Bafarawa.

Amma kasancewar Muhammadu Machunga cikakken barde wanda baida tsoro kuma ya sadaukar rayuwarsa kan assasa addinin musulunci, be razana ba, kuma be juyawa ga kowane bamaguje ba, ya tsaya gam kuma ya shigo har sai da ya kafa kasa wadda ake kira “Wamakko”, wanda kamun zuwansa da kuma jihadin Shehu Usmanu Dan fodiyo ana kiran wannan yanki na garin Wamakko da sunan “Wamakko De Belejoni” Ma’an Dai Shi Ne” Ma’ana Waye Kai ka Tunkaro mu Da Yaki ?”. Tun chan asali mutan Wamakko sullubawa ne da basa razana kuma ba sa tsoron abukkan gaba wanda hakan ya tabbata ga jikansu Sanata Wamakko.

Irin wannan jarumta da zazzafan kishin addini na kakan Sanata Wamakko Muhammadu Machunga, yasa har sai da ya zamo makusanci ga Shehu Usmanu Danfidyo, kuma har yake baiwa Shehu Danfodiyo manyan barade na mayakansa don zuwa jihadin jaddada addinin Allah (SWA) a yankunan Afrika bana Najeriya kadai ba.

Sakamakon gudumuwar da Muhammadu Machunga ya bayar a lokacin yake yake na jihadin Shehu Usmanu Danfodiyo, ya sanya Jagoran Jihadi Shehu Usmanu ya bada sarautar Barade ga yankin Garin Wamakko kuma ga al’ummar kasar Wamakko sannan ga zuri’a ta gidansu Sanata Wamakko. Allahu Akbar !

Amma saboda gujewa shagaltuwa ga mulki ko lamarin shugabanci daga cigaban yada addinin Allah, yasa kakan nashi Sanata Wamakko waton Muhammadu Machunga bai karbi sarautar Barade ba a matsayin Baraden Wamakko, sai ya baiwa dan sa Muhammadu Hafsa jagoranci kuma ya zama matsayin shugaban masarautar Baraden Wamakko. Inda Shima Shehu Usmanu ya ki ya zama Sarkin Musulmi sai ya baiwa dan sa Muhammadu Bello sarautar ta Sarkin Musulmi.

Karshen magana dai sarautar Baraden Wamakko ta gidansu Sanata Wamakko kuma inda asalinsa yake a yanzu haka tana daga cikin sarautu na masu nadin sabon Sarkin Musulmi. Saboda haka Sanata Wamakko yana da cikakken asali da salsala me kyau a jahar Sakkwato kuma kakanninsa tare da Usmanu Danfidyo su ne suka sadaukarda rayuwarsu da iliminsu tareda lokacinsu don kafuwar garin Sakkwato da daular usmaniyya wadda yau muke alfahari da ita da kuma zuwan musulunci a Arewacin Najeriya bayan gwagwarmayarsu da yaki da maguzanci na daular kasar Gobir .

Amma a bangaren shi Attahiru Bafarawa dukkan bayanai na tarihi da salsala sun tabbatarda asalinsa daga yankin maguzawa ne na kasar gobir chan gabas da Sakkwato tun daga tsaga na alamomin diya da jikokin wanda yake kan fuskar shi Bafarawa.

Gaskiyar magana ta Sanata Wamakko cewar shi “Dan ci Rani” ne kamar yanda ya tabbatar da kansa.

Saboda haka har gobe har jibi kuma har duniya ta kare Bafarawa zai tabbata “Dan ci Rani” a jahar Sakkwato ddomin salsalarsa da asalinsa suka tabbatarmasa tun daga kakansa na farko.

Wannan zango bayani na farko kuma sauran bayani na tafe a baya…….

Ra’ayi: Matasa Masu Kishin Sakkwato ne suka wallafa daga Sakkwato.

RELATED ARTICLES

Har yanzu ba labarin mutane 12 da ‘yan bindiga suka sace a Zariya

  . A safiyar Lahadi data gabata  ne aka tashi da wani al'amari maras daɗi a garin Zaria, inda a daren Assabar  'yan bindiga suka shiga...

Mujallar Managarciya na samun ɗaukaka

Mujallar Managarciya da ake bugawa da wallafawa a jihar Sakkwato tana samun tagomashi da ɗaukaka a cikin lamurranta. Mujallar tana fitowa akan takarda bayan wallafa...

Hajjin Bana: Mazauna Saudiya ne kadai aka aminta su gudanar da aikin Hajjin wannan shekara

Gwamantin Saudi Arebiya ta ce jimlar mutum dubu 60 mazauna kasar Saudiya ne kadai za su gudanar da aikin Hajjin wannan shekara ta 2021...

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Har yanzu ba labarin mutane 12 da ‘yan bindiga suka sace a Zariya

  . A safiyar Lahadi data gabata  ne aka tashi da wani al'amari maras daɗi a garin Zaria, inda a daren Assabar  'yan bindiga suka shiga...

Mujallar Managarciya na samun ɗaukaka

Mujallar Managarciya da ake bugawa da wallafawa a jihar Sakkwato tana samun tagomashi da ɗaukaka a cikin lamurranta. Mujallar tana fitowa akan takarda bayan wallafa...

Hajjin Bana: Mazauna Saudiya ne kadai aka aminta su gudanar da aikin Hajjin wannan shekara

Gwamantin Saudi Arebiya ta ce jimlar mutum dubu 60 mazauna kasar Saudiya ne kadai za su gudanar da aikin Hajjin wannan shekara ta 2021...

Rigima ta barke a taron APC na jihar Kano

Rigima ta barke a taron APC na jihar Kano a ranar Assabar. Taron gangamin da aka shirya domin karbar dan takarar gwamnan jihar Kano a...

Recent Comments

ActionScheduler on wc_admin_unsnooze_admin_notes