Spread the love

A jawabin Sanata Mohammed Ɗanjuma Goje a wurin bikin rabon kaya, ya sanarwa al’ummar jihar Gombe zai jingine takarar kujerar siyasa.

“Yan Uwana Alummar jihar Gombe maza da mata zan yi amfani da wannan damar in mika godiyata ta musamman gare ku kasancewar duk wani abun da za a yi wa dan Adam na gata kun yi mini. Na yi takara sau bakwai a jihar Gombe ban taɓa faɗuwa ba, tun ina takara da iyayen gidana, har na dawo ina takara da abokaina, har ta kai ga na dawo ina takara da yaran gidana, na yi takara da World na kada shi aka zo aka hada ni da jikana Nasiru Nono.”

“Lokaci ya yi da zan yi bankwana da shiga takara, don haka daga yau na yi bankwana da yin takara kama daga kan kujerar kansila har zuwa ta Majalisar dattijai, wannan ba wani ya nuni da na yi bankwana da siyasa ba ne takara ne na yi bankwana da ita, za mu cigaba da Siyasa don a siyasa ne za ka Samu damar da za ka taimaki Alumma zamu cigaba da taimakawa”.

Hakan yana nuna kenan a kakar zaɓen 2023 dattijawan ƙasar nan za su janye kansu ga takara su zama masu ba da shawara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *