Spread the loveKungiyoyin matasa sun yi kira kan a Gwamnatin Sokoto ta Sanya hannu da Ido sosai game da Cin Zarafin Mata da ake yi wanda hakan ya sabawa al’ada da addinin musulunci.

Kungiyoyin sun yi kalaman ne a gidan gwamnatin jihar Sokoto a wani tattaki da suka gudanar don nuna rashin gamsuwarsu da abin da ke faruwa yanzu.

Da yake karbarsu Madadin Gwamnatin jihar Sokoto Alhaji Mukhtar Magori ya yi godiya ga wadannan Matasa ga wannan yunkurin nasu kuma gwamnati a Shirye take domin Shiga duk wani Shiri da Matasan suka Kawo.

Da farko amadadin kungiyoyin shugaban taron Sirajo Abdullahi ya ce “Mun zo nan ne domin yin Kira ga Gwamnatin jiha dama ta tarayya gaba daya da a yi dokar hukunci Mai tsanani ga duk Wanda aka Kama Yana Cin Zarafin Dan Adam musamman Mata da kananan Yara” a Cewarsa.

“Addinin Musulunci har Tsuntsu ya Haramta a kashe Idan ba Cinsa Za ka yi ba, ballantana Dan Adam, har akai ga Mace da Musulunchi ya karrama”. a cewar Malam Jamilu Sani Rarah Mai bawa Sarkin Musulmi Shawara kan Kafofin sada zumunta na zamani.Majalisar dukin Duniya ta fitar da Kwana Goma Sha Shidda (16days) domin Nuna Alhini tare da kiraye-kiraye game da Nuna Cin Zarafin jinsin mutum (musamman Mata), a duk Fadin Duniya.

Wannan Ya sanya wata Kungiya da Matasan Sokoto Basu Yarda da Ita ba (Wai da sunan Ita ce Kungiyar da Zasu nuna Alhini ).

Bayan Hana Kungiyar Mai Suna ‘Arewametoo’ wancan yunkuri na Yada Fitsara da lalata tarbiya da sunan nuna Alhini ga Cin Zarafin Jinsi a Jahar Sokoto

Sai Kungiyoyin Matasa jihar Sokoton Suka Shirya gangami da hadin guiwa domin nuna Wannan Alhinin tare da Nunawa Duniya Cewa, Musulunci shi ne Ya Fi cancanta da Nuna Alhini sama da Wani Addini.

Kungiyoyin Matasan dai Sunyi tattaki ne Daga Zabira Mall dake Unguwar gawon nama zuwa Gidan Gwamnatin sokoto.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *