Spread the love

Masoya suna rabuwa ba tare da sun zalunci junansu ba, in masoyiyarka ta yi aure ko masoyinki ya yi auri wata, ba ke ba za ku cigaba da zama abokai tare, saboda kawai kun rabu ba da yaudara ba sai don kaddara.

Rabuwa tana da hanyoyi masu dimbin yawa da ake yinta a tsakanin mutane hakan ya isa ya zama lamarin da zai kai karshen danganta da aka dade ana yi a tare.

Dangantaka tana karewa ba ta hanyar yaudara, zagi, rashin natsuwa da juna da cin amana ba, in haka ya faru zaka iya cigaba da hulda da tsohon masoyinka kenan da ba za ka manta da shi ba.

Huldar kuma ba za ta zama cin amana ba ga wanda kake tare da shi ka rika hulda da tsohon masoyinka, amma wasu na ganin ba komai ba ne akwai manufa mai kyau ta rike huldar don yakan yiwu a taimaki juna wata rana.

Kabiru Nura ya ce tsohuwar masoyiyata na barta kenan in na ci gaba da hulda da ita ban girmama wadda muke tare ba, haba ba zan yi wa matata haka ba, in tana son zama abokinta mi zai hana ta aureni, matata ce abokiyata, ba ruwana da wata can abin da ya faru tsakaninmu ya wuce shi kenan.

Banji ya ce shi kan zai iya wanda yake ganin ba a yin haka bai shiga cikin kasuwanci ba, wasu na yi don zaton za a dawo tare, in ma’aurata na son cutar wani da suke tare da shi za su yi haka.

Munira Yakubu ta ce ana samu in suna aiki wuri daya ko suna karatu amma in ba haka ba suka rike huldarsu cuta ce kawai, kuma bai dace ba in kana son zama da mutum ka aure shi mana amma ka ki, ka je ka auri wani ko kin auri wata amma ku dawo kuna wata cuta da sunan abokai, bai dace ba.

Sadiya Jabo ta ce wannan ai shirme ne da zaluncin zama, wannan maganar da na ji sai da hankalina ya tashi, wai a ce a cikin mutanenmu za a iya samun wannan zalunci da addininmu ke fada shi, ai kowa yasan ba abokantaka tsakanin mata da maza sai da aure amma wasu don biyar bukatar kansu da son yaudara da zalunci su kira wannan wai hulda, sabo ne kawai kuma masu yi yakamata su daina don samun rahamar Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *