Mafiyawan mutane suna tattauna dalilin da ya sa ake samun rikici a auren da mutane ke yi a yanzu saboda mata da yawansu suna aure ne ba tare da wata ƙwaƙƙwarar hujja ba, wani daga cikinsu yana cewa “mafiyawan mata suna aure ne saboda kawai a kira su matan aure, wasu kuwa suna yi ne don a kira su matar wane A ko B, da yawansu ba sa aure saboda so da sadaukarwa.”

A wannan ra’ayin da ya gabatar bai yi magana kan abin da ya sa wasu ke yin auren ba, akwai takura ga dangin mace, wata kuma ganin ta tsufa tana gudun rasa masoyin, wata kuma tana yi ne don tsaro ne a wurinta ka da ta faɗa cikin saɓon zina ko yin juna biyu. Da sauransu.

Halima Abdulmalik mai shekara 38 ta ce t yi aure ne don Allah ya umarci kowace mace ta yi aure don ta cika imaninta, da samun ɗiya da za a kira nata ne nakanta, tana fatan samun nasara yi wa yaranta tarbiya.

Rabi Nura ta ce na auri mijina ne domin saɗaukarwa gare shi ba don komai ba na yi aure don so da sadaukarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *