Spread the love

Ciyamomin jam’iyar APC a jihohi 36 sun ziyarci shugaban ƙasar Nijeriya Muhamnad Buhari a fadarsa dake birnin tarayya Abuja.

Wasu mutane a ƙasar nan suna ganin ziyarar nada nasaba da rikicin da ya mamaye jam’iyar a shugabancinta na jagororin ƙasa.

Ciyamomin suna ƙoƙarin su canja shugabansu na ƙasa Adams Oshiomhole saboda zarginsa da kasawa da hana jam’iyar bunƙasa.

Ana zaton zaman da aka yi an tattauna ne kan lamurran jam’iya don samun haɗin kai ta ƙara ƙarfi a zaɓen 2023 ta yi galaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *