Spread the love

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta yi alkawalin amfani da hukuncin babar kotun tarayya wanda ta umarci gwamnati ta karbo dukkan biyan fanshon da aka yi wa tsoffin gwamnonin da ke aiki, aikin kan mukamin Sanata ko Minista.

Babban Lauyan gwamnatin tarayya ministan Shari’a Abubakar Malami ya ba da wannan tabbacin.

Umarnin na karbo kudin an bayar da shi ne ranar Laraba, Mai shari’a Oluremi Oguntoyinho dake kutun a jihar Lagos a yayin yanke hukuncin karar da ‘yan gwagwarmayar samun ‘yanci da kididdegewa(SERAP) suka shigar a gabanta kan kalubalantar dokar tsarin biyan fanshon tsofafin gwamnoni a jihohinsu da neman kwato kudin da suka karbo don cigaban jama’a.

Malami ya ce gwamnatin tarayya tana tsaye ga kare hakkin jama’a don haka za ta bi umarnin kotu.

Wannan matsayar da ya fitar ta zo ne ta hannun jami’insa kan harkokin yada labarai Dakta Umar Gwandu.

Jiha 21 ne ke da dokoki kan biyan tsofaffin gwamnoni dimbin kudi a matsayin fansho.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *