Spread the love

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin jam’iyar APC gaba ɗayansu a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja.

Buhari ya gana da gwamnonin su kaɗai ba tare da takwarorinsu na jm’iyar PDP ba abin da ke nuna magana ce da ta shafi jam’iyarsu ta APC ba kan shugabancin Nijeriya ne ba.

Managarciya ta yi ƙoƙarin sanin abin da zaman ya ƙunsa sai dai abin ya faskara, har yanzu fadar shugaban ƙasa ba ta fitar da bayani kan zaman ba, an bar jama’a da hasashe da tofa albarkacin baki ga irin tunanin da suke da shi ga tattaunawar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *