Spread the love

Babbar kotun tarayya dake jihar Lagos, a yau Alhamis ta yankewa sanata mai ci kuma tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu hukuncin shekara 12 a gidan yari, bisa zargin sa da yin babakere da naira bilyan 7.65.

Mai Shari’a Mohammed Idris, wanda ya zartar da hukunci, ya bayyana Sanatan a matsayin mai laifi kan tuhumar da ake yi masa tsawon shekaru 12 da suka gabata.

Yanzu kusan shi ne tsohon gwamna na huɗu da ake samu da laifin yin babakere da dukiyar ƙasa, ana kuma zartar masu da hukuncin zaman kaso.

Wannan hukuncin ya ƙara nuna duk wani mutum a ƙasar nan aka kama shi da laifi zai huskanci hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *