Spread the love

Jam’iyar PDP a kudu maso yamma ta zargi ta zargi fadar shugaban ƙasa da yunƙurin karɓe kujerar gwamnan Oyo Seyi Makinde a kotun ƙoli.

PDP ta samu nasara a zaɓen da ya gabata in da ta lashe ƙananan hukumomi 28, APC ta samu biyar kacal.

Wannan yana cikin bayanin bayan taron da msu ruwa da tsaki na jam’iyar a kudu maso yamma suka fitar a zamansu da ya gudana a Abekuta jihar Ogun.

Manyan jam’iyar a kudu da arewa sun halarci zsman.

Jam’iyar ta bayyana hukuncin kotun ɗaukaka ƙara abu ne da yake da rikitarwa mai yawa amma suna fatan a tabbatar musu da nasararsu tun wadda suka samu a wurin zaɓen gwamna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *