Spread the love

Daga Aminu Abubakar Mayanchi, Gusau

Majalisar Sarakunan jihar Zamfara ta yi tir da kuma nuna rashin gamsuwa ga duk wani yunkuri da wasu ‘yan siyasa ke yi na tabbatar an dauke ko sauya kwamishinan ‘yan sandan Zamfara Usman Nagogo.

Wannan bayanin ya fito ne a ta bakin shugaban majalisar sarakunan jihar mai martaba Sarkin Anka Alhaji Attahiru Ahmad a lokacin da yake yi wa manema labarai bayani kan matsayarsu.

Ya ce amatsayinsu na jagororin jama’a sun san al’ada da muhimmanci mutane duk wani yunkuri na dauke kwamishina Nagogo zai iya kawo cikas ga tsaro da zaman lafiyar jihar Zamfara.

“A halin da ake ciki yanzu an yi kokarin samar da tsaro da zaman lafiyar jihar Zamfara an samu sakamako mai kyau, in aka samu nasarar wannan yunkurin ana iya mayar da hannun agogo baya.

“Mutanen jiha sun gamsu da yanda kwamishina Nagogo ke tafiyar da lamarin tsaro tun lokacin da ya zo jihar, musamman yanda ya sanya hikima a wurin tunkarar ‘yan tayar da kayar bai da barayin shanu da mahara da sauran bata gari.” a cewarsa.

Ya yi kira ga shugaban ‘yan sanda na kasa Muhamma Adamu da sauran masu ruwa da tsaki kan lamarin da su fita batun kiran son rai da wasu daidaikun mutane ko kungiyoyi ke yi na a cire Kwamishina Usman Nagogo daga jihar Zamfara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *