Spread the love

Mace shidda a jihar Kebbi sun nutse a kauyen Tindifai yankin Dakin gari a karamar hukumar Suru a jihar Kebbi.

Matan da suka nutse Hadiza Garba mai shhekara 15 da Lauratu Muhammad 13 da Adama Musa 15 da Firdausi Garba 13 da Maryam Abdullahi 13 da Suwaiba Abdullahi 10.

Mutum uku sun tsira in da matukin jirgin dan shekara 13 Umar Faruk ya kubutar da su.

Matan suna kan hanyarsu ne ta zuwa gona wajen dibar shinkafa saman jirgin na katako da zai tsallakar da su suka nutse cikin gulbin dake kusa ga gonarsu.

Ya tabbatar da faruwar lamarin Sakataren yada labarai na Gwamna Abubakar Mu’azu Dakingari, ya ce akwai mace biyar da har yanzu ba a gani ba sun bace cikin ruwan, amma har yanzu ana kan kokari a fito da su kamar yadda aka tsamo sauran matan shidda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *