Spread the love

Gwaman Nasarawa Abdullahi Sule ya koka kan bashin da ya gada ga tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta Tanko Almakura, domin bashin ne ya hana mashi gudanar da gwamnati yanda yakamata.

Ya yi wa al’ummarsa bayani kan lokaci mai wahala da za a shiga a wata shekara ganin yanda harajin jihar ke kilin billin.

Ya nuna takaicinsa ga dimbin bashin da ya tarar wanda tsohuwar gwamnatin ta ci, kuma ta tsara a rika cire kudin daga tushe duk watan Allah.

Gwaman Sule ya fadi hakan ne a wurin taron sanin makamar aiki da aka shiryawa sabbin kwamishinoni a gidan gwamnati dake Lafiya.

Manema labarai sun samu labarin ana biyar jihar sama da biliyan 18(18.9bn), tsohuwar gwamnatin Almakura ta karbi biliyan 8.9 na bail awut a Satumba 2015, gwamnatin kuma ta karbi miliyan 800 domin ta biya albashi da wasu biliyan 10 domin ciyar da jiha gaba.

Almakurra bai yarda da zancen ba ya ce ya biya dukkan bashin da ake biyar jihar har da wasu biliyan 40 da ya gada ana biyar gwamnatin da ya gada, bai bar bashi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *