Spread the love

Daga Jamilu Dabawa, Katsina.

Rundunar ‘yan Sandan jihar Katsina, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan ‘yan sandan Katsina, Sanusi Buba ta yi nasarar damƙe Aisha Abubakar, ‘yar shekara 38 da haihuwa dake Sabuwar Unguwa a ƙaramar hukumar Rimi ta jihar Katsina, bisa zargin kashe ɗiyar Kishiyarta yar shekara huɗu da haihuwa ta hanyar yin amfani da shinkafar ɓera.

Ta baiwa yarinyar abinci bayan cin abincin ne, aka garzaya da ita asibiti, inda likita ya tabbatar da rasuwar ta sakamakon cin abinci mai guba da ta ci.

Da manema labarai suke tambayar wadda ake zargi dalilin da ya sa ta aikata wannan kisan kai, ta bayyana cewa sakamakon rashin jituwar da ke tsakaninta da mahaifiyarta, da kuma kishi ya sanya ta aikata wannan aika-aika, wadda take da ta sani a halin yanzu.

Ana cigaba da bincike, kuma wadda ake zargi ta amsa laifin da ake zarginta na kashe ɗiyar kishiyarta, da zaran an kammala bincike za a kaita kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *