Spread the love

Daga Datti Assalafiy

Bayan doguwar tattaunawa da kamfanonin sadarwar Nigeria suka yi, MTN, Airtel, Glo da 9mobile game da umarnin rage kuɗin sayan data daga kamfanonin sadarwar, kamfanonin sun cimma matsaya game da sabon farashin datan.

Shugaban hukumar kula da harkokin sadarwa (NCC) Farfesa Umar Ɗanbatta ya miƙa wa Ministan sadarwa Dakta Isah Ali Pantami tsarin da kamfanonin suka tsara, sai dai ba’a karanta sabon tsarin a fili ba zuwa yanzu, nan gaba kadan za’a bayyana sabon tsarin da kuma lokacin da za’a fara zartas da shi.

Ministan Sadarwa Pantami ya ce “Kuɗaɗen sayar da Data a Nigeria yayi yawa, kuma yana jawo koma baya wa harkar, abinda zai kawo cigaba wa harkar sadarwa shine data din yayi araha, hakan zai fi jawo hankalin mutane zuwa ga sayan datan, su kansu kamfanonin zasu fi samun kuɗi idan datan yayi araha, tsadar sa kuma zai kore mutane daga sayan datan, wanda hakan koma baya ne.” a cewar Ministan Sadarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *