Spread the love

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce a ƙasar nan yawan fetur da ake amfani da shi ya ragu da kashi 30 kan rufe bododin ƙasa da aka yi.

Shugaba Buhari ya faɗi haka ne a jiya a mahsifarsa Daura a lokacin da yake karɓar a yarin dattawan Katsina, ya ce ba su ayyana wata rana ba haryanzu da za su sake buɗe boda.

Buhari ya yaba matakin da shugaban ƙasar Nijar ya ɗauka na hana ƙasarsa ta zama ma’ajiyar masu sumogalin na kaya don shigowa da su Nijeriya.

A wani bayanin da babban mataimaki na musamman ga Buhari Malam Garba Shehu ya fitar ya bayyana cewa rufe boda da aka yi wata biyu ya kare lagon sumogalin ɗin shinkafa da sauran abubuwan amfani, wannan na cikin yunƙurin gwamnatin Buhari ta bunƙasa harkar noma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *